Amurka Ta Kakabawa Mutane Da Kungiyoyi 18 Takunkumi A Iran

Amurka ta kafa sabon takunkumi a kan wadansu mutane da kungiyoyi 18 na kasar Iran takunkumi, bisa zarginsu da goyon bayan ayyukan makamai masu linzami na Tehran.

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka, ce ta sanar da takunkumin da aka kakabawa wadansu kungiyoyi biyu, da aka danganta da rundunar zaratan sojojin Iran da ake kira Revolutionary Guard, da tace suna da hannu a wajen yin nazarin hanyoyi da kuma kera makamai masu linzami.

Ta kuma ce ayyukan Iran a Gabas ta Tsakiya suna yin “zagon kasa ga dorewar tsaro da kuma ci gaban yankin.”

A halin da ake ciki kuma, ma’aikatar kudin Amurka, ta kakabawa wadansu mutane biyar da kuma cibiyoyi bakwai takunkumi, sabili da goyon bayan sayen kayyakin aikin sojin da Iran tayi, da kuma wadansu Iraniyawa uku da tace suna cikin wata kungiya dake Iran wadda ke aikata miyagun laifuka.

Takunkumin ya haramtawa Iraniyawan amfani da kaddarorinsu dake Amurka, da kuma haramtawa Amurkawa huldar kasuwanci da su.