Kwanakin baya ne shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana yarjejeniyar da aka kulla kan sharuddan shirin mallakar makaman nukiliyar kasar Iran a matsayin "Yarjajjeniya mafi muni da aka taba yi."
Bisa ga dokar Amurka, dole ne Ma'aikatar Harkokin Waje ta sanar da Majalisar Tarayya kowane bayan kwanaki 90, kan halin da Iran ke cike game da kiyaye yarjajeniyar.
Wani babban jami'in gwamnati ya ce kodayake Iran na kiyaye yarjajjeniyar a taikace, amma shakka babu tana saba ma yarjejeniyar bisa manufa, ya kara da cewa gwamnatin Trump na aiki tare da kawayenta wajen daukar tsauraren matakan ganin an aiwatar da yarjajjeniyar.
Babban jami'in na gwamnati ya ce Fadar White house har yanzu ta yi imanin cewa Iran na daya daga cikin gwamnatoci mafiya hadari a duniya, ya yi nuni da goyon bayan da Iran ke baiwa ayyukan ta'addanci, da cigaba da gaba da Isira'ila, da hare-haren internet da ta ke kaiwa Amurka, da kuma yawan take-taken hakkokin dan adam.
Facebook Forum