Amurka Ta Kai Hari Kan Wasu Wurare Mallakin Dakarun Juyin-Juya-Halin Iran A Syria

(FILES) US Defence Secretary Lloyd Austin speaks during a press conference at the NATO headquarters in Brussels, on October 11, 2023.

Wani babban jami’in sojin Amurka ya fadawa manema labarai cewa jiragen yaki kirar F-16 ne suka kai takaitaccen harin a wani rumbun adana makamai a kusa da Abu Kamal.

Sojojin Amurka sun kai hari kan wasu wurare biyu a gabashin Syria mallakin Dakarun Kare Juyin-juya-halin kasar Iran da wasu kungiyoyi masu alaka da su.

Amurka ta kai harin ne da sanyin safiyar ranar Juma’a.

“Wannan takaitaccen hari na kare kai, martani ne ga jerin hare-hare da mafi akasarinsu ba su yi nasara ba da ake kai wa kan ma’aikatan Amurka a Iraqi da Syria, wadanda kungiyoyi da ke samun goyon bayan Iran suka fara kai wa a ranar 17 ga watan Oktoba.” Sakataren Tsaron Amurka Lloyd Austin ya fada cikin wata sanarwa.

“Shugaban Amurka ba shi da wani muradi da ya wuce tabbatar tsaron ma’aikatan Amurka, ya kuma ba da umarnin daukan wannan mataki don nuna cewa Amurka ba za ta lamunci ire-iren wadannan hare-hare ba, za kuma ta kare kanta, da ma’aikatanta da muradunta.” Austin ya kara da cewa.

Wani babban jami’in sojin Amurka ya fadawa manema labarai cewa jiragen yaki kirar F-16 ne suka kai takaitaccen harin a wani rumbun adana makamai a kusa da Abu Kamal.

Sai dai hukumomi ba su ambaci ko an samu jikkata a hare-haren ba.

“Harin ya fada ne kan abin da muka kaikaita,” jami’in ya ce.

Wani babban jami’in ya kara da cewa an kai hari kan dakarun Amurka a Iraqi da Syria da jirage mara matuka da rokoki akalla 19 a ‘yan kwanakin nan.

Muryar Amurka ta tabbatar da aukuwar 17 daga cikinsu.