Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Biden Ya Yi Allah Wadai Da Harin Ba-Zata Da Mayakan Hamas Suka Kai Isra'ila


Biden
Biden

Shugaba Joe Biden, a ranar Asabar din nan, ya yi Allah wadai da harin ba-zata da Hamas ta jagoranci kaiwa, wanda ya kashe daruruwan Isra'ilawa, yana mai cewa abubuwan da suka faru "na fitar hankali ne" kuma "abin takaici ne," kuma "babu dalilinsu" – sannan ya jaddada goyon bayan Amurka ga Isra'ila.

"Yayin da wannan yanayi ke ci gaba da munana, ko shakka babu, Amurka na goyon bayan kasar Isra'ila," in ji shi."

Biden ya ce ya kuma yi magana da Firayim Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu - wanda, kamar dukkan Isra'ilawa da Yahudawa da yawa a duniya, ke kawo karshen mako guda na bikin addini na Sukkot – kuma don isar da wannan sakon, ya kuma tuntuɓi sarkin Jordan da manyan jami'an tsaron kasar Amurka.

Benjamin Netanyahu
Benjamin Netanyahu

Da yake magana daga fadar White House da yammacin ranar Asabar, Biden ya ce tun da farko ya bayyana goyon bayansa karara ga Netanyahu.

"A shirye muke mu bayar da duk abubuwan da suka dace na tallafa wa gwamnati da al'ummar Isra'ila," in ji Biden. Ya kara da cewa, "Ba a taba lamunta da ta'addanci ba. Isra'ila na da 'yancin kare kanta da al'ummarta. Amurka ta yi gargadi kan duk wani bangaren da ke adawa da Isra'ila da ke neman amfani da wannan damar. Taimakon da gwamnatina ke bayarwa don tsaron Isra'ila kwakkwara ne kuma mara gushewa.”

Masu lura da al’amura na cewa makiyan Amurka irin su Rasha da China na kallon wadannan abubuwan da ke faruwa sosai. Kuma a cewarsu, Iran na da hannu dumu dumu.

"Yana da matukar muhimmanci a lura cewa dukkannin wadannan kungiyoyi na da alaka da abu guda, wato Iran,” in ji Joe Truzman, wani manazarci a cibiyar kare dimokradiyya ta mujallar Long War Journal.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG