Hukumomi a Amurka sun kara tsaurara matakan tsaro domin kare wuraren ibadar Yahudawa da Masallatai.
Matakin na zuwa ne yayin da aka gudanar da gangamin nuna goyon bayan Falasdinawa a ranar Juma’a a sassan duniya.
Ko da yake, jami’an tsaron sun yi kira ga jama’a da su ci gaba da harkokinsa na yau da kullum.
Dubun dubatan Musulmi ne suka yi gangamin nuna goyon bayan Falasdinu bayan kammala Sallar Juma’a a sassan yankin Gabas ta Tsakiya.
‘Yan sanda a New York da Los Angeles, birane biyu da suka fi yawan jama’a a Amurka, sun ce za su tsaurara aikin sintirin da suke yi musamman a wuraren ibadan Yahudawa, ko da yake, jami’an tsaron sun ce babu wata alama da ta nuna cewa akwai barazanar kai hari a wuraren ibadan.
Magajin Garin birnin New York Eric Adams, ya ba da umarnin kara tura jami’an tsaro a makarantu da wuraren ibada a matsayin kandarki domin tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a cewar AP.
Matakan da hukumomin tsaron ke dauka a Amurka na zuwa ne yayin da hukumomin Isra’ila ke ci gaba da ba da umarni ga Falasdinawa da ke Zirin Gaza da su fice daga arewacin yankin.
Umarnin na zuwa ne bayan wani harin ba-zata da mayakan Hamas suka kai a kudancin Isra’ila da ya halaka sama da Yahudawa dubu daya.
Hakan ya haifar da martani daga Isra’ilan inda ta yi ta luguden wuta a yankin na Gaza amatsayin ramuwar gayya, wanda shi ma ya halaka sama da Falasdinawa dubu daya.
A halin da ake ciki, mininstan harkokin wajen Iran ya yi gargadin cewa akwai yiwuwar rikicin na Isra’ila da Falasdinu ya yadu a wasu yankunan Gabas ta Tsakiya, muddin Isra’ilan ba ta dakatar da hare-haren da take kai wa yankin Gaza ba.
Ministan harkokin wajen na Iran, Hossein Amirabdollahian, ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar da ya kai shi birnin Bagadaza kafin ya dangana da Beirut, inda daga nan kuma nausa zuwa Damasacus, babban birnin Syria.
Ana dai ta fargabar fadan na Isra’ila da Falasdinu ya fantsama zuwa kan kiyakar Lebanon inda mayakan Hezbollah ke zaman shirin kar-ta-kwana bayan harin da Hamas ta kai a kudancin yankin na Yahudawa.
A ranar Alhamis Isra’ila ta kai wasu hare-hare martani kan filin tashar jiragen saman Damasacus da Aleppo da ke Syria bayan wasu hare-haren da aka kai yankin tuddan Golan Heights da Isra’ila ta mamaye.
Shugaban Amurka Joe Biden, a farkon makon nan ya yi gargadin kada wata kasa ta shiga fadan a yanking abas ta tsakiya, inda ya tura jirgin yakin ruwan Amurka zuwa yankin a matsayin nuna goyon baya ga Isra’ila.
“Barin nanata, duk wata kasa ko kungiya ko wani da ke tunanin amfani da wannan rikici wajen cimma wata manufa, ina da kalma daya da zan fada muku, kada ku kuskura, kada ku kuskura.” Biden ya ce.
Sai dai Ministan harkokin wajen na Iran Amir Abdollahian, ya kalubalanci kalaman na Biden, inda ya ce a daidai lokacin da Amurka take kira da kada kowa ya shiga fadan, a gefe guda kuma ta bari Isra’ila tana ta kashe mata, yara da sauran fararen hula a Gaza.
Dandalin Mu Tattauna