Amurkar ta yi hakan ne don karfafa tabbatar da gwamnatin Iran ta dauki alhakin saba hakkokin bil'adama ta hanyar sanya takunkumi kan wasu karin mutane 10 ‘yan Iran, ciki har da mataimakin ministan hukumar leken asiri na Iran da kuma wasu manyan kwamandojin rundunar Iran ta musamman da ake kira IRGC, da kuma karin wani kamfanin Iran."
An sanya takunkumin ne don auna daidaikun 'yan Iran da kamfanonin Iran da ke da alaka da zalunci da murkushe masu zanga-zangar lumana da hukumomin Iran ke yi.
Daga cikin mutanen da Amurka ta kakaba wa takunkumin har da wasu manyan jagororin rundunar IRGC, da madugu wajen aikata zaluncin kan masu zanga-zangar: Mohammad Nazar Azimi da Karoush Asiabani.
"Azimi da Asiabani ne ke jagorantar rundunar IRGC da ake zargi da aikata wasu munanan abubuwa da jami'an tsaron Iran suka yi tun farkon zanga-zangar."
Wadannan abubuwan sun hada da harbin masu zanga-zangar da ba sa dauke da makamai da harsasai, da kuma harbin motocin da ke kokarin kai jakkunan jini don wadanda suka jikkata a asibitocin yankin.
"Duk duniya na kallo, kuma a shirye duniya take ta dauki matakin mayar da martani kan tashin hankalin da jami'an Iran suke haddasawa kan al'ummarsu."
"Idan Iran na ci gaba da aikata laifukan take hakkin bil Adama, za mu ci gaba da matsa ma ta lamba."
"Za mu ci gaba da goyon bayan 'yan Iran wadanda suka yi tsayin daka don kare hakkinsu, a karkashin jagorancin mata jarumai – yayin da su ke fuskantar danniya."