Amurka Ta Gargadi Ghana Kan Dokar Haramta Luwadi

Auren jinsi daya

Amurka ta gargadi Ghana da cewa idan har ta kuskura ta amince da dokar hana luwadi da madigo, to dangantakar kasuwanci da zuba jari tsakaninsu za ta yi tsami.

Jakadiyan Amurka Virginia E. Palmer ce ta bayyana hakan yayin wata ganawarsu da manema labaru inda ta bayyana cewa, “Ghana kasa ce mai maraba da kowa kuma akwai karfin dangantaka da fahimtar juna tsakanin addinai, akwai kuma jituwa tsakanin kabilu. Hakan ya sa Ghana ta kasance kasa mai ƙarfi da sha'awa ga masu zuba jari.

Ina fata ya kasance haka da al'ummar LGBTQI. Amma idan aka nuna bambanci ga'yan luwadi da madigo a Ghana, ba masu zuba jari da 'yan luwadi kawai zai aika da sigina ba, harda sauran kamfanonin Amurka. Sa'an nan Ghana ba za ta samu karbuwa gun masu jari ba. ina fatan za ta kasance cikin wadanda Amurka zata yi maraba dasu wajen kasuwanci,” inji ta.

Virgina E.Palmer da Shugaban Ghana Akufo

Ambasada Palmer ta kuma kara da cewa yayin da wasu kamfanoni na Amurka ke shirin saka hannun jari a Ghana, duk wata doka da ke nuna kyama ga 'yan luwadi da madigu na iya cutar da martabar kasar a matsayin kasar da masu zuba jari ke sha’war zuwa.

Wani rahoton da sashen kasuwanci ta kasar Amurka wa fitar ya nuna cewa, a shekarar 2022 Ghana ta samu kimanin dalan Amurka biliyan 1.8 sakamakon fitarda kayayyaki irinsu gwal da cocoa da danyen mayi zuwa Amurka.

To sai dai matakin katse huldar kasuwanci tsakanin Amurka da Ghana sakamakon dokan haramcin luwadi da madigu da dangoginsu zai iya sanya Ghana cikin halin kunci musamman yayinda kasar ke fama da matsalar kariyan tattalin arziki, inji Shuaib Abubakr masanin tattalin arziki.

Shi kuwa babban Jami'in a Cibiyar Ci Gaban Demokraɗiyya (CDD-Ghana), Michael Augustus Akagbor, ya yi tambaya game da ikon yin shawarwari na Ghana a matakin kasa da kasa yayin da ake tunanin zartar da wannan kudiri na yaki da luwadi. Yace "ya kamata Ghana ta tantance matsayinta da tasirinta a matakin duniya kafin yanke wasu shawarwari na samarda dokar haramcin luwadi da madigo.”

Abdul Mannan Muhammad na daya daga cikin shugabannin kungiyoyinda suka gabatarda kudirin dokar a majalisa dokoki na bukatar da a haramta luwadi da madigo ya kuma ce babu ruwa ko iska da zai hana su haramta luwadi duk da barazanar da Amurka bazai keyi.

Har yanzu dai gwamnatin kasar Ghana ba ta bayyana matsayin ta akan wannan magana ba. Bisa tsarin dokar dai da ake shirin aiwatar wa a Ghana, za'a daure duk wadanda aka kama da laifin luwadi ko madigu da zama gidan yari har na tsawon shekaru goma, sannan shekaru uku kuma ga duk wanda ya bayyana yanayin luwadi ko madigo.

Saurari rahoton Hamza Adam

Your browser doesn’t support HTML5

Amurka Ta Gargadi Ghana Kan Dokar Haramta Luwadi