Jiya Talata Amurka ta fara tuntunbar kawayenta akan shirye shiryen yiwuwar fadada aiyukan soja a kasar Syria biyo bayan mumuman harin makamai masu guba da ake zargin Syria ta kai akan wani kauye dake hannun yan tawaye.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka Heather Nauert tace Amurka na duba yiwuwar maida martanin hadin kai ko hadin gwuiwa a kasar Syria. Shugaban Amurka Donald Trump yayi kashedin cewa za’a dauki mataki mai tsanani akan dukkan wadanda suke da alhakin kai hari a gabashin Ghaouta a ranar Asabar data shige da ya kashe akalla mutane arba’in.Cikin ‘yan kwanakin da suka shige, shugaban na Amurka yayi ta zantawa da takwarorin aikinsa na Britaniya da Faransa akan wannan batu.
Tuni dama shugaban na Amurka ya dorawa shugaban Syria Bashar Al Assad da kasashen Iran da Rasha, kasashen dake goyon bayan Syria, laifin wannan hari. Shugaba Assad ya musunta wannan zargi.
Jiya Talata Rasha ta hau kujerar naki akan daftarin shirin da Amurka ta tsara ko kuma ta gabatarda nufin kafa wani kwamitin da zai binciki wannan hari.
A saboda nazarin irin martani ko kuma matakin da za’a dauka ne Fadar shugaban Amurka ta White House tace shugaban na Amurka ba zai kai ziyarar kasashen Amurka ta kudu kamar yada aka shirya a wannan makon ba.
Maimkon sa mataimakin sa zai kai ziyarar domin halartar taron kolin kwanaki biyu da za’a yi a kasar Peru a ranar sha uku ga wannan wata idan Allah ya kaimu