Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ta yiwu, “bayan abin da ya faru,” gwamnatinsa ta bayyana shawarar da ta yanke akan yadda za ta maida martani, gameda abinda ake kyautata zaton harin guba ne aka kai a wajen Damascus, babban birnin Siriya.
“Za a dau fansa, kuma fansa mai tsanani,” a cewar Trump bayan ganawarsa da manyan jami’an sojan kasar jiya litinin da maraice.
Ya jaddada abinda ya kira ikon da Amurka ke da shi na dakatar da zalunci, kamar na harin da aka kai ranar Asabar a gabashin garin Ghouta da ‘yan tawaye suka mamaye, harin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 40.
Trump ya ce mu na da hanyoyi dayawa da zamu maida martani, “yin amfani da karfin soja,” a cewar Trump ba tare da yayi karin bayani ba. A shekarar da ta gabata Trump ya bada umurnin akai hare-hare ta sama a akan wani sansanin jiragen sama na Siriya inda aka taba kaddamar da wani harin guba.
Facebook Forum