Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Ya Dorawa Shugaban Rasha Alhakin Harin Guba Akan Syria


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya dorawa Shugaban Rasha Vladimir Putin alhakin harin guban da aka kai Syria tare da lashe takobin cewar za'a ga babbar sakayya

Shugaban Amurka Donald Trump a jiya Lahadi ya dora wa shugaban Rasha Vladmis Putin da kuma Iran laifi game da harin guba na rashin imanin a Syria da ya kashe akalla mutane 40, yayin da ya lashi takobi cewar za a ga babbar sakayya.


A wani tofin Allah tsine na ba saban ba a kan shugaban Rahsa, Trump ya fada cewar shugaba Putin na Rasha da Iran sune suke da laifi, domin baiwa Assad da ya kwatanta da dabba goyon baya, yana nufin shugaba Syria Bashar al-Assad.


Kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya zai yi zama a yau Litinin a kan zargin kai harin, bayan kasashe tara suka bukaci shirya taron gaggawa a kan haka. Kungiyar Tarayyar Turai tace akwai shedar dake nuni cewar gwamnatin Syria zata sake kai sabon harin guba.

Amma kuma kafofin yada labarum kasar Syria, sun bada rahoton wani harin makami mai linzami da aka kai da sanyin safiyar yau Litinin akan wani sansanin soja a lardin Homs, suna masu fadin cewa akwai wadanda suka jikatta.

Rahotanin sunce an auna harin ne akan sansanin T4 kuma sun dorawa rundunar sojan Amirka laifin kai harin. Jami’an Amirka sun musunta cewa Amuka ce ta kai wannan harin.

.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG