Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawan Amurka Ta Bukaci Kamfanin Facebook Ya Kare Bayanan Jama'a


Shugaban kamfanin Facebook, Mr. M. Zukerberg, yayinda ya bayyana a gaban kwamitocin bincike na majalisun Amurka
Shugaban kamfanin Facebook, Mr. M. Zukerberg, yayinda ya bayyana a gaban kwamitocin bincike na majalisun Amurka

Jiya Talata shugaban kamfanin sada zumunta na Facebook Mr Zukerberg ya bayyana a gaban kwamitocin bincike na majalisun dokokin Amurka akan yadda wani kamfani ya yi amfani da bayanan miliyoyin mutane lokacin zabe

Wakilan Majalisar dattijan Amurka a jiya Talata suka bukaci a kare bayanan mutane yadda ya kamata a dandalin sada zumuncin Facebook. Wakilan sun bukaci haka ne a lokacin da wasu kwamitocin Majalisar dattijan Amurka guda biyu suka yiwa shugaban kamfanin Mark Zuckerberg tambayoyi sosai akan yadda ake amfani da bayanan miliyoyin jama’a ba bisa ka’ida ko da izininsu ba.

Shugaban kwamitin shari’a na Majalisar dattijai, Chuck Grassley dan jam’iyar Republican daga mazabar jihar Iowa yace ko tantanma babu ba’a yiwa masu amfani da dandalin adalci ba. Mr Zuckerberg yace kuskurensa ne kuma yana neman a gafarta masa.

Yayi alkawari cewa za’a kare bayanan mutane yadda ya kamata. Haka kuma yayi magana akan alfaharin yadda ake sada zumunci tsakanin jama’a a dandalin na Facebook.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG