Amurka ta bada sanarwar shirye shiryen sake aza takunkunmin masu gauni akan bangaren makamashi da harkokin bankin kasar Iran, tana mai fadin cewa akwai bukatar gwamnatin Iran ta canja halayar ta ko kuma take taken ta, ta zama kamar sauran kasashen duniya.
Direktan tsara manufofi a ma’aikatar harkokin wajen Amurka Brian Hook shine yayi wannan furuci jiya litinin a tattauna da yan jarida.
Mr Hook ya bukaci kasar Iran ta mutunta abubuwan da aka nema ta yi domin ta zama abinda yace, kamar sauran kasashen duniya.
Yace a ranar shidda ga watan gobe na Augusta Amurka ke shirin aza takunkun farko. Wadannan takunkunmin zasu auna bangaren cinnikayar motoci da zinari da kuma wasu muhimman karafa. Yace sauran takunkunmin kuma Amurka zata aza su ne a ranar hudu ga watan Nuwamba idan Allah ya kai. Su kuma zasu auna bangaren makamashi da man fetur da kuma harkokin banki.