Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Zargi Koriya Ta Arewa da Habbaka Tashar Nukiliya a Boye


Shugaba Trump da Shugaba Kim
Shugaba Trump da Shugaba Kim

yayin da duniya ke farincikin alkawarin yin watsi da makaman nukiliya da Koriya Ta Arewa ta yi, sai kuma ga shi wata kungiyar na waswasin hakan.

Wata kungiyar saka ido ta ce hotunan tauraron dan adam sun nuna cewa a watannin baya-bayan nan, an yi matukar inganta daya daga cikin tasoshin nukiliyar Koriya Ta Arewa.

Kungiyar 38 North, wacce ke sa ido kan harkokin soji, da harkokin tattalin arziki, da harkokin zamantakewa da dai sauransu a Koriya Ta Arewa, ta fada a wani rahoto ranar Laraba cewa hotunan da aka dauka daga sararin sama ranar 21 ga watan Yuni sun nuna cewa Koriya Ta Arewa ta dada inganta tashar nukiliyarta ta Yongbyon.

Hukumar leken asirin tabbatar da tsaron kasa ta Amurka CIA ta ki cewa komai kan wannan rahoton kuma Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce ita ba ta magana kan abin da ya shafi bayanan sirri. Fadar Shugaban Amurka ta White House ta ki cewa komai da aka tuntube ta.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG