Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

BAKIN HAURE: Ma'aikatar Shari'ar Amurka Ta Kalubalanci Hukumcin Kotu


Wata mace tana rike da danta a kan iyaka
Wata mace tana rike da danta a kan iyaka

Ma'aikatar tsaron Amurka tace hukumcin da wani alkali a jihar California ya yanke kan batun raba bakin haure da 'ya'yansu zai kara dagula lamari ne kawai

Gwamnatin shugaba Trump tace hukumcin da wani alkali ya yanke da ya umaraci gwamnati ta sada iyaye bakin haure da ‘ya’yansu wadanda aka raba a kan iyakar kasar Amurka zai sa a tsare kananan yaran a na lokaci mai tsawo fiye da yadda ake yi a halin yanzu.

Ma’aikatar shari’a ta bayyana a cikin wata takarda da ta shigar a kotu jiya jumma’a cewa, “gwamnati ba zata raba iyalai ba, amma zata tsare su tare a lokacin da ake tantancesu bayan an kamasu suna kokarin keta kan iyaka zuwa Amurka.

Yana yiwuwa a tsare iyalai na tsawon watanni ko ma shekaru sabili da dubban takardun bakin hauren da suke jibge a kotu da ba a samu kaiwa garesu ba sabili da yawansu.

Wata dokar kotu da ake kira yarjejeniyar Flore ta hana a tsare kananan yara fiye da kwanaki ishirin.

Alkalin wata kotun Amurka a birnin San Diego na jihar California ya yanke hukumci cewa, tilas ne a gama iyayalan da aka raba cikin kwanaki talatin, a kuma maida kananan yara ga iyensu cikin makonni biyu.

Jami’ai sunce kimanin kananan yara dubu biyu ne suke jira a gamasu da iyayensu

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG