Shugaban Amurka Donald Trump ya kare hukumar da ke sa ido kan shige da ficen kasar mai cike da takaddama, inda ya soki kiran da wasu ‘yan adawan jam’iyyar Democrat ke yi na a rushe hukumar.
A wata hira da ya yi da gidan tabjin na Fox News a jiya Lahadi, shugaba Trump ya ce, a siyasance, “yana kaunar batun na shige da fice.”
Ya kara da cewa, idan har ‘yan Democrat suka ci gaba da kiran a rushe hukumar “yana ganin ba za su kara cin wani zabe ba.”
Dubun-dubatar masu zanga zanga ne suka yi bore a ranar Asabar a sassan Amurka, kan tsarin “ba-sani-ba-sabo” da yake aiwatarwa inda ake cafke duk wanda ya shiga Amurka ta kan iyakar Mexico ba bisa ka’ida ba, sannan ya nemi da a yi hanzarin sake hada ‘ya’yan bakin haure sama da dubu-biyu da iyayensu da aka raba, a lokacin da suka shiga Amurkan.
Facebook Forum