Amurka Ta Aza Takunkumi Kan Kamfanonin Kasar Pakistan 7

Wilbur L. Ross, ministan kasuwanci na Amurka

Amurka ta aza takunkumi kan kamfanoni 23 na wasu kasashe da suka hada da bakwai daga Pakistan akan zargin suna fataucin makaman kare dangi

Ahalinda ake ciki kuma, Amukra ta aza takunkumi kan kamfanonin kasar Pakistan 7, kan zargin suna fataucin makaman kare dangi.

Wani reshen ma'aikatara cinikayya ta Amurka da ake kira BIC a takaice shine ya dauki wannan mataki kan kamfanoni 23, guda 15 daga Sudan , daya daga Singapore, sannan da karin bakwai daga Pakistan a bakin kundinta. Amurka ta hakikance Kamfanoni da suke cikin wannan kundi suna aiki da ya saba muradun Amurka ta fuskar tsaro da manufofin ta na kasashen ketare, kamar yadda shafin reshen ma'aikatar a internet ya yi bayani.

A gefe daya kuma, ministan tsaron Pakistan ya ce dangantakar da Amurka take so da kasar shi ne ta fuskar aikin soja kadai, maimakon danganataka ta mutuntawa wadda idan akwai matsala data taso za'a zauna a nemi bakin zaren warwareta.

Ministan tsaron Khurram Destgir, ya gayawa Muryar Amurka cewa saboda haka ne yanzu dangantaka tsakanin kasar da babbar kawarta China ya kara zurfi, yayinda Islamabad take kara kusantar Rasha.