Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Ya Dora Haraji Akan Kayan China Dake Shigowa Kasar


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Jiya Alhamis shugaban Amurka Donald Trump ya amince da kara haraji akan kayayyakin China dake shigowa Amurka da adadin kudinsu ya kai dalar Amurka dubu miliyan sittin a shekara

Shugaban Amurka Donald Trump ya rattaba hannu a kan wata kasida ko kudurin shugaban kasa a jiya Alhamis, da zai fara daukar matakai na dora haraji a kan jerin kayayyaki daga China da yawansu suka kai 1,300, da suke shigowa Amurka da kudinsu ya kai dala biliyon 60.


Wannan mataki zai takaitawa China zuba jari a masna’antun fasahar Amurka, wanda hakan zai janyo kwatankwacin yaki ta fuskar cinikayya da China.


An yanke shawara haka sakamakon bincike da hukumar cinikayyar Amurka ta gudanar domin tabbatar da ko China na gudanar da harkokin kasuwancinta yanda yakamata ko kuma tana nuna ha'inci ga Amurka.

Bayan binciken watanni bakwai, ofishin wakilin Amurka ta fuskar ciniki ya gano cewa manufofin kasuwancin China sun saba ka'idar cinikayya.


A wurin sanya hannu a kan yarjejeniyar, Trump yace Amurka tana da fasaha da dama da ake sacewa.


Ya kuma dora laifin gibi da Amurka ke samu a huldan kasuwancinta da China wanda a zamaninsa ya kai dala biliyon 375.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG