Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Bayyana Kasashen Da Ba Za Su Biya Karin Haraji Ba


Shugaba Donald Trump
Shugaba Donald Trump

Bayan korafe-korafe da kuma fargabar yiwuwar a shiga kazamar gasar cinakayya tsakanin wasu kasashe da Amurka, yanzu Fadar Shugaban Amurka ta White House ta ce za a tsame wasu kasashe daga jerin masu biyan harajin kayan sayarwa.

Fadar Shugaban Amurka ta White House, jiya Alhamis, ta bayar da sanarwa game da kasashen da za ta tsame na wani dan lokaci, daga jerin kasashen da za ta saka haraji kan karafa da dalmarsu, da za a fara aiwatarwa daga yau Jumma’a.

A farkon wannan watan ne Shugaba Donald Trump ya bayar da sanarwar saka haraji da kashi 25% kan karafan da ke shiga Amurka da kuma harajin kashi 10% kan dalmar da ke shiga Amurka.

Kasashen da za a saurara masu na wani dan lokacin sun hada da Argentina da Brazil da Canada da Mexico da Koriya Ta Kudu da kuma mambobin kungiyar Tarayyar Turai.

Fadar White House ta ce ta na kan tattaunawa da dukkannin kasashen da ta tsame su din kuma za ta rinka sa ido kan yadda wadannan kasashen ke shigo da kafaransu da kuma dalmarsu.

Shugaba Trump zai tsai da shawara ranar 1 ga watan Mayu kan ko zai cigaba da tsame kasashen ko a’a, bisa ga yadda tattaunawar da ake yi da su ta kaya. Kungiyar EU za ta shiga tattaunawar a madadin mambobinta.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG