Amurka Na Shirin Kara Runduna A Kan Iayakarta Da Mexico

Shugaba Donald Trump

Ma’aikatar tsaron Amurka tace tana niyar aika karin sojoji dari uku a kan rundunar Amurka dake aiki a kan iyakar kudancin kasar da Mexico a aikinsu da zai basu daman kusanci da bakin haure, lamarin da ya sabawa tsarin farko na dakarun da ya hanasu kusanci da bakin haure.

Ma’aikatar Sojin Amurka ta Pentagon ta fada a jiya Juma’a cewa karin sojojin 300 zai hada ne da masu dafawa sojoji abinci da zasu rika dafawa bakin haure abinci da sauran jami'ai da zasu yi ayyuka da dama kamar direbobin bos da zasu jigilar bakin haure dake tsare.

Wannan mataki ya sha bamban da tsarin Amurka wanda ya hana sojoji yin mu’amala kai tsaye da bakin haure.

Mai magana da yawun Pentagon Charlie Summers yace tun da yake jami’ansu zasu dafawa bakin hauren abinci, toh dole ne zasu samu kusanci dasu.

Sai dai yace sakataren tsaro mai riko Patrick Shanahan bai riga ya sanya hannu a kan wannan bukatar karin sojoji da ma’aikatar tsaron cikin gida ta Homeland Security tayi, amma anasa ran zai yi haka.

Tun da farkon wannan wata, shugaban Amurka Donald Trump yace zai bukaci karin sojoji a kan iyakar kasar da Mexico.