Shugaban Amurka Donald Trump, jiya Litinin, ya ruga kotu, don hana wani kwamitin majalisar tarayyar Amurka bayar da sammacin gabatar masa da bayanan da su ka shafi shi Trump kansa da kuma harkokin kasuwancinsa, daga wani kamfanin aikin akanta, wanda ya shafe shekara da shekaru yana masa aikin akanta.
Dan majalisar wakilai, Elijah Cummings, wanda shi ne shugaban Kwamitin Bincken Al’amura, na bukatar bayanai na tsawon shekaru 10 game da Trump daga kamfaninsa.
Amma shugaban kasar da rukunin kamfanoninsa, sun fada a karar da su ka shigar ta hadin gwiwa cewa, “sammacin bayyana irin wadannan bayanan abu ne da bai yiwuwa, saboda ba abu ne da ya shafi harkokin majalisa ba.”
Karar da Trump ya shigar ta kara da cewa, “a maimakon ‘yan jam’iyyar Dimokarat su hada kai da Shugaban kasar wajen aiwatar da harkoki na bai daya da za su amfani Amurkawa, sun fi dukufa wajen bincike-bincike don su samu abin da za su iya amfani da shi wajen ji ma shugaban kasa a siyasance.
Facebook Forum