Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamitin Majalisa Ya Bukaci a Ba Shi Cikakken Rahoton Mueller


Shugaban kwamitin harkokin da suka shafi shari'a a majalisar dokoki, Jerry Nadler
Shugaban kwamitin harkokin da suka shafi shari'a a majalisar dokoki, Jerry Nadler

A wani taron manema labarai da ya gudanar, kakakin shugaba Vladimir Putin, Dmitry Peskov, ya ce har yanzu ba su amince da wannan zargi ba.

Rahoton Robert Mueller kan katsalandan din da Rasha ta yi, na kara gaskata abin da jami’an tattara bayanan sirri Amurka na yanzu da wadanda suka shude suka yi ta fada, bayan zaben shugaban Amurka a shekarar 2016.

Ko da yake, akwai wasu da ke cewa, ya kamata rahoton na Mueller da ma’aikatar shari’ar Amurka ta fitar a ranar Alhamis, ya zama gargagadi kan cewa yunkurin da hukomomin Moscow ke yi na kassara tsarin dimokardiyyar Amurka, na nan yana ci gaba da fadada, inda kusan za a iya cewa sun yi nasara.

Sai dai a jiya Juma’a, jami’an Rasha, sun ci gaba da musanta zargin cewa sun yi yunkurin yin shisshigi a zaben Amurka na 2016n, inda suka yi biris da daruruwan shafukan rahoton na Mueller da suka nuna hujjar cewa Rashan, ta sa hannun a zaben.

A wani taron manema labarai da ya gudanar, kakakin shugaba Vladimir Putin, Dmitry Peskov, ya ce har yanzu ba su amince da wannan zargi ba.

A jiya juma’a ne, shugaban kwamitin majalisar dokokin Amurka mai kula da fannin shari’a, Jerry Nadler, ya aika da takardar neman a ba su cikakken rahoton da kwamitin binciken na Mueller ya gudanar.

"Ya zama wajibi majalisar dokoki ta samu rahoton wanda ba a tace ba, hade da hujjojin da kwamitin bincike na Robert Mueller ya gano.” Inji Nadler.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG