Shekaru biyar kenan bayan da Nijer din ta sake rungumar wannan tafarki.
Sanarwar wace aka rarabawa ‘yan jarida ta fara da cewa kasar Amurka na goyon bayan tafarkin demokradiyar dake gudana cikin yanayi na kwanciyar hankali da adalci domin hakan ne kawai ke bada damar a shirya zabe na gaskiya mai ‘yan takara da yawa.
Saboda haka ne gwamnatin Amurkata yanke shawarar bada gudunmowa a shirye shiryen zabubukan da Nijer ta sa gaba. Alal misali ofishin jakadancin Amurka a Nijer da hukumar USAID sun dauki alkawalinkebe dala miliyan kusan 2 da rabidomin shirye shiryen zabe a kasar .
Daga cikin aiyukan da za’a yi ta hanyar anfani da wadanan kudade akwai maganar jan hankalin jam’iyun siyasa su gane mahimmancin maida hankali akan batutuwan da suka shafi bukatun talakawan kasar Nijer sannan a wani shirin hadin gwuiwa hukumar USAID da kungiyar WANEP zasu dage a aiyukan riga kafin kaucewa tashe tashen hankula a lokutan zabe ta hanyarsamarda bayanan abubuwan dake faruwa a yankunan karkara akai akai domin tabbatar da cewa al’amura na tafiya cikin ruwan sanyi a yayin zabubukan na badi.
Sanarwar ta ofishin jakadancin Amurka a Yamai ta kara da cewa Amurka ta dauki dawainiyar wani ayarin aiyukan waye kan matasa ta hanyar kungiyar YALI domin fadakar da al’ummar Nijer domin zaburarda matasa su shiga da dimbin yawa a dama da su a dukkan zabubukan da za’a gudanar a shekarar 2016.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5