Sakamakon korafe korafen da jama’ar Nijar ke yi akan rashin cin moriyar shirin bada magani kyauta ga mata masu juna biyu da yara kanana ne ya sa gwamnatin kasar bada umurni gudanar da bincike don gano gaskiyar lamari.
Binciken wanda aka gudanar a jihohi 5 daga cikin 8 na kasar ya gano cewa gwamnati da jami’an kiwon lafiya kowa na da hannu wajen tauye tafiyar wannan shiri da ke da manufar tallafawa talakawa.
Malan Abubakar Maiyaki, jami’i a ma’aikatar kididigar jamhuriyar nijer ya yi karin bayani. Yace abinda suka binciko ya nuna cewa, jami’an dake aiki a cibiyoyin basu aiwatar da shirin bisa tsari. Banda haka kuma ana bukatar gwamnati ta rika biyan likitoci kudin da aka sayar da magani domin su samu su sake sayen wani magani da shi. Saboda haka yace akwai bukatar duba bangaren gwamnati da kuma likitoci domin kowanne yayi aikinshi yadda ya kamata.
Bisa ga bayanan malaman kiwon lafiya, rashin fahimtar tsarin tahiyar wannan shiri daga bangaren al’uma na daga cikin dalilan da suka haddasa cikas wa dorewarsa.
Bayanai na cewa bashin miliyan kusan dubu 20 ne asibitoci ke bin gwamnati a matsayin kudaden magungunan da aka baiwa talakawa kyauta a karkashin wannan shiri yayinda a daya gefe ake zargin wadansu asibitocin da laifin rubuta farashin da ya zarta na magungunan da suke bayerwa a zahiri lamarin da ake ganin shine masababin tsayarwa wannan shiri a galibin asibitoci mallakar gwamnati.
Ga rahoton da wakilin muryar amurka SULE MUMUNI BARMA ya aiko mana daga Yamai.