Yayin da zabukan kasar Nijar ke kara karatowa, ‘yan adawa na zargin jam’iyya mai-ci da shirin magudi, wanda ya hada da bai wa masu unguwanni (ko barumai, kamar yadda ake kiransu a janhuriyar Nijar) turamen atanfa da kudi don su goyi bayan jam’iyyar mai ci.
Jagoran ‘yan adawa a Damagaram, Mamman Sale y ace a bai wa kowani baruma jakka biyu da turmin atanfa biyu. Y ace ana bin mataki-mataki ne wajen kokarin sa shugabannin jama’a su goyi bayan magudi. Ya ce da farko sun fara nuna cewa hadin kai shugabannin su ke so don zaben ya yi nasara, babu mamaki cewa a mataki nag aba a bukaci baruman su goyi bayan yin magodi.
To saidai kuma wani baruma Abdulsalam Jibirillu, magatakartan kungiyar Barumai a Damagaran,y ace wannan al’amarin ya kada su. To amma y ace babu ruwan kungiyar Barumai cikin wannan al’amarin. Ya ce sam ba dukkannin Barumai ba ne aka yi wannan abin assha da sub a. Don haka, in ji shi, za su kiran taron Barumai su bada kashedi.
To amma kakakin Jam’iyyar PNDS-Tarayya mai mulki Sani Sabo, y ace sam babu wani Baruman da aka tattauna da shi cewa idan an zo zabe ya goyi bayan PNDS-Tarayya. Ya ce ko da ma hakan gaskiya ne, bas u ne farau ba.