A Jamhuriyar Nijer kungiyoyin yaki da dokar kisan kai sun kaddamar da wani littafi da za a yi anfani da shi wajen wayarda kan masu bakin fada-a-ji a kasar a game da rashin canacantar zartas da hukuncin kisan kai.
A albarkacin shagulgulan ranar yaki da hukuncin kisa ta duniya da aka saba gudanarwa a kowace ranar 10 ga watan Oktoba ne wadanan kungiyoyin kare hakkin dan Adam suka kaddamar da wannan littafi da zummar fahimtar da ma’ikanta a mataki daban daban rashin dacewar raba dan Adam da rayuwarsa komenene tsanantar laifin da ya aikata. Alhaji Mustapha Kadi Umani na kungiyar CODDAE ya bayyanacewa sun kiyaye duk wani abinda zai kawo sabani ga tsarin zamantakewar al’umawajen hada wannan littafi.
Mustapha Kadi ya kara da cewa kundin tsarin mulkin Nijer ya haramta raba dan Adam da rayuwarsa saboda haka ya yi kira ga hukumomin kasar sun dakatar da hukuncin kisa.
A cewar wadanda suka hada wannan littafi kafafen yada labarai na da babbar rawar da zasu taka wajen soke dokar hukuncin kisa a Nijer saboda haka aka dorawa ‘yan jarida nauyin wallafawa domin jama’a su fahimci illar zartas da hukuncn kisa a kasar da ta rungumi salonmulkin demokradiya.
Ga karin bayani.