Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Taron Fannonin Dokokin Tsarin Mulki a Nijar


Mr.Morou Amadou Ministan Harkokin Shari'ar Nijar
Mr.Morou Amadou Ministan Harkokin Shari'ar Nijar

Wasu kasashen Afirka da suka hada da Senegal da Benin da Afirka ta Kudu da Faransa suna taron kwana uku akan fannonin dokokin tsarin mulkin kasa a Jamhuriyar Nijar

A jamhuriyar Nijar kwararru a fannin dokokin tsarin mulki daga kasashen Afrika da na Turai sun soma wani taron nazari akan tsarin ayyukan kotunan tsarin mulki da zummar bullo da wani kundin da zai taimaka a shayo kan matsalolin da ke dabaibaye shara’ar rigingimu ‘yan siyasa.

Kasar Nijar na cikin kasashen da bangarorinsiyasa ke yawan shigar da karan juna a gaban kotun tsarin mulki domin a warware wani kullin da ya kawo cijewar al’amura walau a tsakanin adawa da masu rinjaye a majalisar dokoki ko kuma a tsakanin majalisar dokoki da bangaren zartarwa. Dalili kenan da kungiyar ANDC ta masanan dokokin tsarin mulki ta ga dacewar shirya wannan taro.

Sau tari a kan zargin alkalan kotunan tsarin mulki a kasashen Afrika da nuna bangaranci musamman taka rawa da bazar masu mulki wajen yanke hukunci .

To ko wace gudunmawa wannan taro zai bayar domin kawo karshen irin wannan tunani ? Dr MAINA BUKAR KARTE Kwarar ren masani ne na dokokin tsarin mulki.

An dai gayyato ‘yan farar hula da ‘yan siyasa a wannan haduwa cikinsu har da ABUBAKAR SABO wakilinjam’iyu masu mulkin Nijar.

Taron na tsawon kwanaki 3 na matsayin wani fagen mahawarar kwararru daga jamio’in kasashen Senegal Cote D’ivoire, Benin, Burkina Faso, Afrika ta Kudu,Nijar da Faransa.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:25 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG