Babban wakilin Amurka a tattaunawar zaman lafiya da ake yi a Afghanistan, ya gana da shugabani a Kabul jiya Lahadi bayan ya saukarsa kasar, a wata ziyara ba zata, wadda ita ce ta farko da ya kai tun bayan da shugaban Donald Trump, ya dakatar da tattaunawa da kungiyar 'yan tawayen Taliban kan yadda za a kawo karshen yakin Afghanistan.
Jami’ai sun ce Zalmay Khalilzad ya samu rakiyar wasu jami'ai, ciki har da Lisa Curtis, babbar darakta mai kula da Kudanci da Tsakiyar nahiyar Asiya a kwamitin Tsaron Amurka.
Ziyar ta na zuwa ne a ranar da hukumar zabe mai zaman kanta ta Afghanaistan (IEC) ta tsaida ranar 14 ga watan Nuwamba mai zuwa a matsayin ranar da za a saki sakamakon wuccin gadi na zaben shugaban kasar mai cike da takaddama da aka yi ranar 28 ga watan Satumba.