Shugaban Amurka Donald Trump ya ce an kashe shugaban kungiyar ISIS Abu Bakr al-Baghdadi bayan wani farmaki da dakarun Amurka na musamman suka kai a Syria.
“A daren jiya Amurka ta yanke hukunci akan shugaban kungiyar ‘yan ta’adda na daya a duniya, abinda Trump ya sanar kenan daga fadar White House a yau Lahadi.
Shugaban ya kara da cewa “babu sojan Amurka ko daya da aka rasa a farmakin da aka kai” amma an kashe mayakan Baghdadi da yawa.
Trump ya kuma ce shugaban na kungiyar ISIS wanda ya boye a wasu ramukan karkashin kasa yayi kokarin tserewa, kuma ya yi ta kyarma, da kuka da kuma ihu. Trump ya kuma ce Baghdadi ya tarwatsa kansa da wata rigar nakiya da ya sanya, har ya kashe wasu yara su uku.
Rahotanni sun bayyana cewa farmakin da aka kai a lardin Idlib dake Syria ya hada da jiragen sama masu saukar ungulu, da wasu jiragen, ciki harda marasa matuki na Amurka.
A watan Yulin da ya gabata wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadin cewa manyan shugabannin kungiyar ISIS na cikin wadanda suka kutsa yankin Idlib.
An dai sha yin kuskuren bada rahoton mutuwar Baghdadi lokuta da yawa a baya.
Facebook Forum