WASHINGTON D.C. —
Hukumomi a jihar California, sun gargadi sama da mutum miliyan 25 da ke zaune a arewaci da kaudancin jihar, da su zauna cikin shirin ko-ta-kwana, yayin da bala’in wutar daji ke ci gaba da ruruwa a yankin.
Bushasshiyar iska da ke kadawa, ta sa masu ayyukan kashe gobara na fuskantar matsala wajen shawo kan wutar.
A ranar Larabar da ta gabata, wutar dajin ta lakume garin da ake kira Geyeserville a yankin Sonoma Country, lamarin da ya tilastawa kusan mutum dubu biyu ficewa daga gidajensu.
A kuma ranar ta Larabar ce, kamfanin wutar lantarki na Pacific and Gas, ya fara kashe wutar lantarkin wasu yankunan jihar, gudun kada turakun wuta su fadi su haifar da wata wutar.