Amurka Da Pakistan Zasu Hada Kai Don Samar Da Zaman Lafiya a Afghanistan

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya gana da sabbin shugabannin gwamnatin Pakistan, inda bangarorin biyu suka amince zasu sabunta matakai domin inganta dangantaka tsakanin su data tabarbare, sannan su hada hanu domin ganin an samu zaman lafiya a Afghanistan.

Dangantakar dake tsakanin Amurka da Pakistan, wadanda a hukumance kawaye ne a yaki da ta’addanci, ta samu matsala a shekarar da ta gabata, kan zargin cewa Pakistan tana taimakawa ‘yan kungiyar Taliban domin a ci gaba da samun tashin hankali a kasa makwabciya watau Afghanistan.

Sakatare Pompeo, wanda babban hafsan hafsohin sojan Amurka, Janar Joseph Dunford, ya rufawa baya a wannan ziyara, sun yi wata ganawa da Ministan harkokin wajen Pakistan Shah Mehmood Qureshi. Daga bisani kuma jami’an na Amurka sun gudanar da wani taro daban daban da Fara Minista Imran Khan, da Janar Qamar Javed Bajwa, babban hafsan hafsohin sojin Pakistan.

Babban jami’in diplomasiyar Amurka ya bi a hankali wajen nuna kwarin gwiwarsa, game da yadda sakamakon ganawar tasu zata kasance.