Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Wallafa Littafi Kan Rashin Iya Shugabancin Trump


Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa, kalaman da aka Ambato da kuma labaran da aka wallafa a wani littafi a kan shugabancinsa, kage ne dake cike da nufin damfarar jama’a.

Littafin da aka rubuta dangane da shugabancin Trump, da wani dan jarida da ake dorawa alhakin sauke shugaba Richard Nixon daga karagar mulki, ya bayyana gwamnati mai ci a matsayin wadda take neman kifar da kanta da kanta, da kuma rudani cikin watanni goma sha tara na farko da kafa gwamnatin.

Littafin da ake kira “Tsoro: Shugaba Trump a fadar White House, mai shafi dari hudu da arba’in da takwas, da Bob Woodward ya rubuta,wanda za a fitar ranar goma sha daya ga wannan watan na Satumba, ya bayyana cewa, mataimakan shugaban kasa suna satar takardun bayanai a kan teburinsa da kuma daukar wadansu matakai da nufin yiwa shugaban kasa yankan baya.

Littafin ya bayyana Trump a matsayin wanda bai san abinda ke faruwa a kasashen duniya ba, da kuma fadar dake cike da kurakurai da kuma mummunan rashin jituwa tsakanin mukarraban shugaban kasa.

A sakon da ya buga a shafinsa na twitter jiya Talata da yamma, shugaba Trump ya kuma nemi sanin ko Woodward sojan hayar jam’iyar Democrat ne.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG