Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Gargadi Siriya Da Rasha Da Kuma Iran


Donald Trump
Donald Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya gargadi kasashen Siriya da Rasha da kuma Iran, a wani sakon da ya tura ta kafar ‘Twitter’ jiya Litini, cewa akul su ka yi abin da ya kira, “babban kuskuren da ka iya haddasa matsalar jinkai” ta wajen kai hari kan lardin Idlib da ke hannun ‘yan tawayen Siriya.

Tunda da farko a jiya Litini din, Iran ta nuna goyon bayanta ga wani shirin da Siriya ke yi na kai harin sake kwato ‘yanki daya tilo da ya rage a hannun ‘yan tawayen, ta na mai cewa ya kamata a kakkabe wadanda ta kira ‘yan ta’adda daga yankin Idlib na arewa maso yammacin Siriya.

Ministan Harkokin Wajen Iran Mohammed Javad Zarif ya je Dimashku jiya Litini don ganawa da takwaran aikinsa da kuma Shugaba Bashar al-Assad.

A halin da ake ciki kuma mutumin da shugaba Donald Trump ke so ya zama babban Alkalin Kotun Kolin Amurka, alkalin kotun tarayya Brett Kavanaugh, na iya fuskantar tambayoyi masu tsanani kan batutuwa dabam-dabam yayin tantance shi a Majalisar Dattawa a yau dinnan talata, ciki har da matsayinsa kan zubar da ciki da luwadi da kuma ikon shugaban kasa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG