Amurka da Burtaniyan sun fidda takardun gargadi ga yan kasashen nasu
biyo bayan mummunan harin ta'addanci da aka kai gidan gyaran hali
na koje dake yankin babban birnin Tarayyar Najeriya
Abuja, Najeriya —
Amurka ta shaidawa Amurkawan dake Abuja cewa akwai yiwuwar kara samun matsalolin tsaro a ciki da wajen yankin babban birnin tarayyar kasar,saboda haka dole su yi kaffa kaffa da takatsantsan har nan da makonni biyu masu zuwa.
Bugu da kari Amurka ta bukaci 'yan kasar nata da su guji bin kan hanyar filin jirgin sama na Abuja, inda ta nanne garin kuje yake ganin sha'anin tsaro na kara sukurkucewa a Najeriya, yana da kyau a guji yankunan da ake tababar amincinsu.
Kazalika ita ma Burtaniya taja hankalin 'yan kasarta da su yi taka tsantsan ganin yadda matsalar tsaron ke shiga wani sabon babi, inda tace su kuma guji yin bulaguro zuwa wasu jihohin kasar goma sha tara da ma na yankin Naija Delta.