Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Boko Haram Sama Da 60 Ne Suka Gudu A Harin Gidan Yarin Kuje – Magashi


Bashir Salihu Magashi
Bashir Salihu Magashi

Yayin da yake ganawa da manema labarai kwana guda bayan harin, Magashi ya ce gidan yarin na Kuje na dauke da ‘yan Boko Haram 64.

Ministan tsaron Najeriya, Bashir Salihu Magashi, ya ce dukkan mayakan Boko Haram da ake tsare da su a gidan yarin Kuje sun tsere.

A ranar Talata, wasu ‘yan bindiga suka kai hari gidan yarin na Kuje wanda ke Abuja, babban birnin Najeriya.

Yayin da yake ganawa da manema labarai kwana guda bayan harin, Magashi ya ce gidan yarin na Kuje na dauke da ‘yan Boko Haram 64.

Ya kara da cewa, ga dukkan alamu ‘yan ta’adda ne suka kai wannan hari a gidan yarin, inda suka ta da bama-bamai don su kubutar da mambobinsu.

“Akwai alamu da ke nuna cewa Boko Haram ne, domin muna da su da dama a tsare a nan.” Gidan talbijin na Channels ya ruwaito Magashi yana fada.

Ya kara da cewa, a halin yanzu, ba a san inda ko da yansu ('yan Boko Haram) yake ba amma an yi nasarar cafke wasu fursunoni 600 daban da suka yi yunkurin gudawa.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG