Amurka Tayi Kira Ga China Kan Iyakar Tekun Kudancin China

Tekun Kudancin China

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry yace, Amurka na kira ga kasar Sin da makwabtanta na gabar tekun Pacific a yankin Asiya, da su nemi hanyar cimma mafita a diflomasiyyance don warware rikicin iyakar tekun Kudancin China.

Kerry ya bayyana haka ne a yau Litinin a lokacin bude taron shekara-shekara karo na 8 game Tsarawa da kuma Tattaunawar Tattalin Arziki tsakanin Amurka da kasar Sin. Ya kuma yi kiran ne domin ankarar da yadda ake fargabar rikicin yanki ta gabar tekun.

Yankin da kasashe da dama suke ikirarin mallakinsu ne. kasashen da suka hada da Taiwan da Vietnam da Philippines da Brunei da kuma Indonesia. Yankin akalla hada-hadar kudaden da suka kai Dalar Amurka Biliyan 5 ke ratsawa.

Haka kuma an yi ammannar wajen na da isashshiyar rarar man fetur da iskar gas. Hakan ce ta sa kasashe ke tada girar sama ga kasar Sin na yadda ta ke girke sansanin sojinta a fakaice bisa shirin ko ta kwana.