Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sai An Nemi Dabaru Masu Inganci Domin Sasanta Rikici Tsakanin Isra'ila Da Palasdinu


John Kerry
John Kerry

Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry, ya ce ana bukatar dabaru masu inganci wajen samar da sulhu ga rikicin Isra’ila da Palasdinu.

Kerry ya yi wannan jawabi ne a safiyar yau Asabar, bayan da ya hadu da ministan harkokin wajen Faransa, Jean-Marc Ayrault a birnin Paris, gabanin ya kama hanyarsa ta zuwa Mongolia.

Shi dai Kerry ya kai ziyara kasar ta Faransa ne, inda ya gana da kasashe fiye da 20 wadanda suka nuna shirinsu na marawa yunkurin da Faransa ke yi, na tsara hanyoyin kawo karshen rikicin Isra’ila da Palasdinua nan da karshen shekarar nan.

Babu dai wani wakili da ya halaraci taron daga bangarorin biyu da ke takaddama da juna.

A jiya Juma’a, Kerry ya ce akwai bukatar Isra’ila da Palasdinu su dauki matakan gaggawa wajen nuna cewa a shirye suke su samar da zaman lafiya mai dorewa.

Wadanda suka halarci taron sun nuna cewa tsare-tsaren da ke kasa na sasanta rikicin ba su is aba, sun kuma nuna bukatar a samar da hanyoyin shawo kan matsaloli irinsu su hare-hare da ake kaiwa, da kuma gine-gine da ake yi a wuraren da basu dace, wadanda a cewarsu su ke kara fadada rikicin.

XS
SM
MD
LG