A wani gangami da mafi akasarin su matasa ne suka yi yau Laraba a fadar gwamnatin jihar Sokoto, Gwamna Aminu Waziri Tambuwal, ya sanar da cewa ya sauya sheka daga APC zuwa PDP.
Gwamna Tambuwal ya bayyana wasu dalilai masu yawa da suka sa ya kai ga yanke shawarar canza jam’iyya. Cikin dalilansa ya ce a baya ya dawo shiga APC ne saboda alkawarin da aka yi musu na cewa za a kawo gyara ga wasu lamuran kasar dake tafiya ba dai-dai ba, amma sai gashi hakan bai samu ba.
Tambuwal ya bayyana cewa duk alkawuran da aka yiwa ‘yan kasa da su ‘yan siyasa babu wani abu da aka cika, illa dai gwamnati na tafiya kara zube matsaloli na ‘kara ci gaba, haka kuma ‘yan Najeriya na ‘kara shiga cikin wahala.
Masu lura da al’amuran siyasa jihar Sokoto sun dade suna sharshi kan wannan al’amari. Yanzu haka dai ana ganin cewa gwamnan zai fuskanci kalubale guda biyu, na farko shine abokin tafiyarsa Sanata Aliyu Wamakko zai ci gaba da kasancewa a jam’iyyar APC, na biyu kuma shine irin magoya bayan da shugaban Najeriya Buhari ya ke da shi a jihar Sokoto.
Domin karin bayani saurari tattaunawar Maryam Dauda da Murtala Faruk Sanyinna.
Your browser doesn’t support HTML5