Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Jarida Zasu Iya Shawo Kan Yayata Labaran Kage:Amanda Bennett


Direktar Muryar Amurka Amanda Bennett
Direktar Muryar Amurka Amanda Bennett

Yau ce rana ta biyu da Shugaba Muryar Amurka ke ziyara a Najeriya inda ta gana da Ministan Watsa Labarai da kuma Shugabanin Kungiyar Yan Jaridu na Kasa Mata da Maza

Abinda yafi daukar hankalin taron shine batun labaran kage da ake yayatawa yanzu kamar wutar daji da yasa mutane suke gaza banbanta sahihan labarai da kuma kanzon kurege da ake yatatawa ta kafofin sadarwa.

Da yake jawabi a wurin taron, ministan watsa labarai Lai Mohammed yace mahukuntan kasar sun tashi tsaye wajen ganin cewa sun shawo kan matsalar, tare da magance rigingimu da wannan matsalar ta labaran karya ke haifarwa., musamman ta yanar gizo.

Yace wannan zaman ya samar masu da damar sake jawo hankalin kafofin watsa labarai na gida da kuma waje kan labaran da ake yayatawa a kan Najeriya. Yace daga kasashen ketare ana gani kamar akwai rarrabuwar kawuna a Najeriya ta fannin addini da kabilanci, amma yace ba haka abin yake ba.

A nata jawabin, Darektar Muryar Amurka Amanda Bennett ta bayyana cewa, tashar tana kokarin gudanar da aikinta bisa tsarin aikin jarida, inda Muryar Amurka ke watsa labarai masu muhimmanci tare kuma da kare gaskiya, ta kuma ce Najeriya na cikin kasashe a Afrika da Muryar Amurka ke girmamawa, tare da karfafa dangantaka da aka shafe shekara da shekaru ana morewa. Uwargida Bennett tace yadda za a iya magance matsalar yayata labaran karya shine a samar da isassun sahihan labarai. Ta kuma jaddada cewa, Muryar Amurka zata tabbatar da gudanar da aikinta bisa la’akari da doka da ka’idar aikin. Ta kuma sanar da shirin kaddamar da wani sabon shirin talabijin na mata a watan Oktoba da zai maida hankali kan batutuwa da suka shafi kasashen Afrika.

Ita ma a nata jawabin, shugabar kungiyar ‘yan jaridu mata ta Najeriya Ify Omowole ta nemi hadin kan Muryar Amurka wajen yayata fafatukar mata, musamman wadanda suke niyar tsayawa takara.

Saurari cikakken rahoton Madina Dauda

Ganawar Amanda Bennett da 'yan jaridun Najeriya-2:02"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:03 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG