Shugaban majalisar dattijan ya buga a shafinsa na twitter cewa, "ina so in sanar da 'yan Najeriya cewa, bayan kyakkyawar tuntuba na yanke shawarar barin jam'iyar APC.
Bukola Saraki, ya bayyana cewa, yana la'akari da cewa, alhakin dubban mutane ya taraya a wuyansa da suka hada da magoya bayansa da abokan arziki da na siyasa da suke dogara ga jagorancinsa, sai dai tura ta kai bango kasancewa duk wani yunkurin sulhu da zaman lafiya da kuma ci gaban da suke nema ya cimma tura.
An jima ana radi radin cewa, shugaban majalisar dattijan yana shirin sake sheka bayan jimawa suna takun saka da wadansu jami'an gwamnati.
Tuni jam'iyar PDP da kuma wadansu kusoshi a jam'iyar da suka hada da tsohon mataimakin Najeriya Atiku Abubakar da ya bayyana niyar tsayawa takarar shugabancin kasar karkashin tutar jam'Iyar PDP suka yaba matakin da shugaban majalisar dattijan ya dauka.
Zamu ci gaba da kawo maku ci gaban da aka samu kan wannan batu.
Facebook Forum