Da yake kaddamar da dokar da cibiyar sa ido da kare al’umma ta gabatar, yace za a bi tsarin sau da kafa , a kuma hukumta wadanda suka saba dokar da ake kira PBoR a takaice.
Mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa, ana fuskantar kalubala matuka a fannin lafiya a Najeriya sabili da haka wannan dokar zata taimaka wajen cimma gurin gwamnatin na ganin dukan ‘yan kasa sun sami kula a fannin yadda ya kamata.
Ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya tana daukar batun kula da lafiyar al’umma da muhimmanci, dalili ke nan da yasa ta kebe kashi daya cikin dari na kudin shiga da zata samu a shekara ta dubu biyu da goma sha takwas domin kula da ayyukan jinya.
Dokar ‘yancin marasa lafiyan ta kunshi kare ‘yancin marar lafiya a muhimman fannoni goma sha biyu da suka hada da ‘yancin samun bayanan asibiti, da ‘yancin bayanin kudin jinya, da ‘yancin samun kulawa mai inganci, da ‘yancin korafi da bayyana rashin gamsuwa da yadda aka yiwa marar lafiya jinya.
Sauran fannonin da ya shafi ‘yancin marar lafiya sun hada da ‘yancin samun kulawar gaggawa, da ‘yancin kin amincewa da jinya, da kuma ‘yancin amincewa ko kin amincewa da shiga gwajin magunguna ko jinya.
Facebook Forum