Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Chibok Sun Ce Gwamnatin Najeriya Ta Yi Biris Da Batun Ceto 'Yan Matan Da Suka Rage


Mahaifiyar wata daga cikin 'yan matan Chibok da aka sace
Mahaifiyar wata daga cikin 'yan matan Chibok da aka sace

Sun bayyana hakan ne a yayin wata ganarwasu da Shugabar Muryar Amurka, Amanda Bennet wadda ta kai ziyara Najeriya.

Shugabar ta gana da al’ummar garin Chibok ciki har da iyayen wasu daga cikin ‘yan matan Chibok da aka sace inda suka yaba da kokarin da Muryar Amurkan ke yi wajen jan hankali game da batun musamman kan ceto ‘yan matan da suka rage a hannun ‘yan Boko Haram.

Korafin ‘yan kungiyar ya hada da zargin cewa gwamnatin Najeriya ta daina batun ‘yan matan Chibok kuma ba ta sanya su a cikin duk wata tattaunawa don ceto su.

Sai dai ‘yar majalisar dattawa, Binta Masi Garba da ta halarci ganawar ta ce ba hakan maganar ta ke ba, musamman wannan zargin cewa gwamnati ta yi biris da batun ‘yan matan makarantar Chibok.

Asabe Benita Bashir, ita ce ‘yar majalisa mai wakiltar yankin da ya hada da Chibok a majalisar dokokin tarayya, ta ce za su ci gaba da daukar mataki da ya wajaba wajen gano dukkanin matan.

Shugaban kungiyar al’ummar Chibok na Abuja, Nkeki Mutah ya ce ba za su daina fitowa don nemo 'yan matan ba har sai dukkan su sun dawo gida.

Shugabar Muryar Amurka Amanda Bennet, ta ba da tabbacin ci gaba da yada labarun nemo matan don tabbatar da adalci.

Hakanan ta dauki wani faifai bidiyo inda ta aika sako kai tsaye ga al’ummar kasashen duniya su hada kai wajen yaki da ‘yan ta’adda don dawo da ‘yancin wadanda a kan sace da jefa rayuwar su cikin garari, musamman 'yan matan Chibok.

Saurari cikakkiyar rohoton

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:50 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG