Hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa NEMA, ta gargadi kananan hukumomi da jihohi da su zauna cikin shiri duba da yiwuwar aukuwar ambaliyar ruwa a wasu sassan kasar.
Cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na Facebook a ranar Litinin, hukumar ta yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su kasance sun kimtsa duba da yawan ruwan saman da aka yi hasashen za a gani bana.
Hukumar ta ce tuni ta ankarar da manyan ofisoshinta da ke Legas, Ibadan, Ekiti, Abujam Minna, Jos, Enugu, Owerri, Fatakwal, Edo, Uyo, Kano, Sokoto, Kaduna, Maiduguri, Yola da Gombe da su zauna cikin shiri.
“Babbar Darektar NEMA, Zubaira Umar ta sa ofisoshin da ke shiyyoyin kasar da su zauna cikin shiri tare da yin aiki da hukumomin jihohi da suke.” Sanarwar ta ce.
A watan Afrilun bana gwamnatin tarayya ta fitar da sanarwar jihohi 31 da za su iya fuskantar matsalar ambaliyar ruwa.
“Jihohin sun hada da Akwa-Ibom, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Benue, Borno, Cross River, Delta, Ebonyi, Edo, Imo, Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Kogi, Kwara, Lagos, Nasarawa, Niger, Ogun, Ondo, Osun, Oyo, Filato, Rivers, Sokoto, Taraba da Yobe.” Ministan albarkatun ruwa da tsabtace muhalli, Prof Joseph Utsev ya ce a farkon shekarar nan yayin wani taron manema labarai.
Ministan ya kara da cewa a tsakanin watannin Afrilu da Nuwamban bana ne za a iya fuskantar matsalar ta ambliyar ruwa a sassan na Najeriya.