Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Guguwa Tafe Da Ruwan Sama Mai Yawa Sun Sauka Jihar Florida


Guguwa a jihar Florida, Amurka
Guguwa a jihar Florida, Amurka

Ambaliyar ruwa da guguwa mai karfi sun shafi sassan kudancin jihar Florida da yawa a ranar Laraba, lamarin da ya sa hanyoyi suka cika da ruwa, abinda ya kawo cikas ga ‘yan wasan kwallon hockey na Florida Panthers da ke kan hanyar zuwa gasar cin kofin Stanley da za a yi a Canada.

WASHINGTON, D. C. - Guguwar da ta taso daga yankin tekun Mexico na kara dannawa a fadin jihar Florida, kusan a daidai lokacin da aka shiga lokacin guguwa a farkon watan Yuni, wanda a wannan shekara ake hasashen yanayin zai yi muni fiye da yadda aka gani a baya, a daidai lokacin da kuma ake nuna damuwa kan cewa sauyin yanayi na kara wa guguwar karfi.

Hanyoyi da dama sun cika makil da ababen hawa. A kan babbar hanyar Interstate 95 da ke garin Broward, an sauya inda ababen hawa ke bi don kaucewa wa wani wuri da ruwa ya mamaye kuma masu aikin kwangila da ke kula da hanyoyi na kan hanyar zuwa fara aikin janye ruwan da ya cika magudanun ruwa a yankin, a cewar hukumar sintirin manyan hanyoyi ta jihar Florida a wani sakon imel.

Ba za a sake bude babbar hanyar ba har sai an janye ruwan, a cewar hukumar.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG