Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Tarayya Ta Zayyana Jihohin Da Ka Iya Fuskantar Ambaliyar Ruwa

Jihar Imo
Jihar Imo

Ruwan sama babu kakkautawa da ake samu a baya-bayan nan ya sabbaba ambaliya a wasu jihohi da birnin tarayya Abuja, al’amarin daya sanya Ministan bukatar gwamnatocin jihohin kasar su tsananta kokarin da suke yi na yashe magudanan ruwa.

Gwamnatin Najeriya tayi gargadin cewa karuwar ambaliya da cigaba da saukar ruwan sama na iya kara ta’azzara annobar kwalarar da ake fama da ita a kasar.

Ministan Albarkatun Ruwa da Tsaftar Muhalli Joseph Terlumum ne ya bayyana wannan damuwa a jawabinsa ga manema labarai a yau Alhamis.

A cewarsa, zuwa Laraba 3 ga watan Yulin da muke ciki, mutane dubu 2 da 102 sun kamu da kwalara sannan ta hallaka 63 tun bayan barkewar annobar.

Ruwan sama babu kakkautawa da ake samu a baya-bayan nan ya sabbaba ambaliya a wasu jihohi da birnin tarayya Abuja, al’amarin daya sanya Ministan bukatar gwamnatocin jihohin kasar su tsananta kokarin da suke yi na yashe magudanan ruwa.

A cewar ministan, har yanzu babu daya daga cikin madatsun ruwan dake ciki da wajen Najeriya da aka saki.

Ya cigaba da cewa daga watan da muke ciki ake sa ran koguna su fara tumbatsa, kuma jihohin da ake ganin al’amarin zai shafa sun hada da; Akwa Ibom da Anambra da Adamawa da Benue da Bayelsa da Cross River da Delta da Edo da Jigawa da Kogi da Kebbi da Kaduna da Niger da Nassarawa da Ondo da Ogun da Rivers da Taraba da kuma birnin tarayya, Abuja.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG