PLATEAU, NIGERIA - Haka kuma a karamar hukumar Quan Pan, ambaliyar ruwa ta shafe gonaki, gidaje da gadoji.
A unguwannin Gangare da Rikkos da ke karamar hukumar Jos ta Arewa ma, ambaliyar ta kwashe gadar da ta hada yankunan biyu, amma tuni shugaban karamar hukumar, Shehu Bala Usman ya sake gina gadar, don hana aukuwar wani ibtila’in.
Tsohon kansila a yankin Nyelleng a karamar hukumar Pankshin, Sudan Bako ya ce karfin ruwa dake saukowa daga tsaunukan dake kewaye da kauyukan, shine ke haddasa ambaliya da lalata gadoji.
Daraktar Hukumar Wayar Da Kan Jama'a Ta Kasa reshen Jihar Filato, Madam Kaneng Pam-Hworo ta ce hukumar na ci gaba da wayar da kan jama’a don su dauki matakan kare kansu daga illar ambaliya.
A Jihar Binuwai ma, fiye da gidaje dari ne ambaliyar ruwa ta shafa, kamar yadda shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta Jihar, Emmanuel Shior ya shaida wa manema labarai.
Darakta a ma’aikatar muhalli ta Jahar Filato, Sunda ‘Danbaki ya bukaci jama’a da su rika bin umurnin hukumar yanayi ta kasa.
A kowace shekara dai, Najeriya na asarar makudan kudade, dalilin ambaliyar ruwa, tana kuma shafar lafiyar al’umma da muhalli dake bukatar hukumomi su maida hankali a kai, don rage barnar da ambaliya ke janyowa a kasar.
Saurari cikakken rahoton daga Zainab Babaji:
Your browser doesn’t support HTML5