Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Ta Ja Hankali Kan Yiwuwar Aukuwar Ambaliyar Ruwa A Wasu Jihohin Kasar


Wani yankin da aka yi ambaliyar ruwa a jihar Jigawa
Wani yankin da aka yi ambaliyar ruwa a jihar Jigawa

Shugaban hukumar ya kara da cewa suna sa ido kan lamarin a lokacin da ake tunkarar watannin da kuma ci gaba da sa ido kan hukumomin kasar Kamaru dangane da aukuwar ambaliyar ruwan.

Hukumar kula da albarkatun ruwa ta Najeriya ta yi hasashen cewa za’a samu ambaliyar ruwa a daga karshen watan Agusta zuwa farkon watan Satumba na shekarar 2021 a jihonin Rivers da babban birnin tarayya Abuja.

Shugaban hukumar Inginiya Nze Clement Onyeaso ne ya fadi hakan a wata ganawa da ya yi da manema labarai a Abuja, inda ya bayyana cewa yankunan da aka yi hashen ambaliyar ruwa za ta shafa a baya-baya nan tare da yankunan da suke kusa da Kogin Niger da Benue, za su fara samun mummunar matsalar ambaliyar ruwan daga karshen watan Agusta.

Shugaban hukumar ya kara da cewa suna sa ido kan lamarin a lokacin da ake tunkarar watannin da kuma ci gaba da sa ido kan hukumomin kasar Kamaru dangane da aukuwar ambaliyar ruwan.

Mista Eze ya kuma gargadi mazauna Jihar Legas su guji cike hanyoyin ruwa na kogin Atlantik tare da gina unguwanni akai kamar yadda akayi a unguwar Lekki da Tsibirin Banana saboda yin hakan zai iya haifar da babbar matsala anan gaba.

Eze ya kuma yi kira ga yan Najeriya musamman Gwamnatocin Jihohi ta su kasance cikin shirin ko ta kwana ta hanyar tabbatar da tsaftace magudanan ruwa.

Tun da farko hukumar tayi hashen za’a samu mummunan ambaliyar ruwan kananan hukumomi 121 na jihohi 27 da suka hada da Lagos, Nasarawa, Anambra, Abia, Kwara, Kaduna, Enugu, Borno da kuma Ondo sakamakon yawan ruwan sama da rashin ingantaccen mugudanar ruwa.

Najeriya dai ta kasance a yankin Kogin Niger da ya kunshi kasashe tara da suka hada da Benin, Burkina Faso, Kamaru, Chadi, Cote d’ivore, Guinea, Mali, da Nijar, sai kuma Najeriyar da ta kasance daga bangaren gangaren kogin wanda idan sauran kasashen sun sami ambaliya, to zata fisu shiga mawuyacin hali.

XS
SM
MD
LG