Al’umomin jamhuriyar Nijar na ci gaba da kiraye-kiraye ga 'yan siyasa da ma al'umar Najeriya baki daya don kaucewa dukkan wata tarzomar dake da nasaba da rikicin zabe tare da jan hankulan 'yan Nijar mazauna Najeriyar su nisanci kansu da shiga dukkan wata harkar da ta shafi zaben na Najeriya.
Lura da zazzafan kalaman wasu daga cikin 'yan siyasar ta Najeriya a yayin yakin zaben da aka kammala a jiya Alhamis ya sa 'yan Nijar jan hankulan bangarorin siyasa akan bukatar su yi karatun ta nutsu don ganin komai na wannan zabe ya gudana cikin kwanciyar hankali.
Saboda haka nuna halin dattako ya zama wajibi ga kowane dan Najeriya, Hajiya Zara Maina, wata tsohuwar 'yar jarida ce dake bin diddigin harakokin siyasar Najeriya. Ta ce samun tashin hakali a Najeriya ya shafi mutanen Nijar.
Kamar yadda doka ta haramtawa kowane mutun tsoma hannunsa a harakokin siyasar kasar da ba ta shi ba, ya sa wani mai sharhi akan al'amuran yau da kullum Ibrahim Amadou, tunatar da 'yan Nijar mazauna Najeriya nauyin da ya rataya a wuyansu game da zaben na 16 ga watan Fabareru.
A yadda wannan zabe ke daukan hankalin jama'ar Nijar Shuwagabanin addinai sun dukufa ga addu’oin zaman lafiya tare da gargadin matasa su nisanci duk wani dan siyasar da zai yunkura amfani da su don tayar da bore akan maganar zabe.
Domin karin bayani saurari rahotan Sule Muminu Barma.
Your browser doesn’t support HTML5