Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Jaddada Bukatar Gudanar Da Zaben Najeriya Cikin Lumana


Amurka ta jaddada bukatar dake akwai na gudanar da zabe cikin lumana da kwanciyar hankali a Najeriya.

Jakadan Amurka a Najeriya Stuart Symington, ya kara jaddada bukatar gudanar da babban zaben Najeriya cikin kwanciyar hankali da lumana, ya kuma ce kowanne dan Najeriya zai dauki alhakin abin da ya fada ko ya aikata, domin duniya ta saka ido akan Najeriya.

Jadada Symington ya kara da cewa yana fatan duk abin da kowa zai yi zai saka kishin ‘kasa da son kasar, musamman hankoran ganin ta samu kyakykyawan makoma.

Masu sharshi kan al’amuran yau da kullum, irin su mallam Ali Abdullahi ya ce wannan kira na Amurka abin a yaba ne.

Da yake bayyana dalilan da ya sa Amurka da kungiyar tarayyar Turai ke nuna zakuwa a zaben Najeriya, farfesa Mohammed Turkur Baba, ya ce tun zaben da aka yi na shekarar 2015, sun nuna sha’awar cewa a yi zaben Najeriya cikin lumana da adalci, ganin irin girman kasar ne ya sa hankali ke kan ta.

Saboda yawan jama’ar da Najeriya ke da ita da kuma arzikin kasa, ya sa manyan kasashen duniya ke dari-dari da wani abu da zai faru, domin idan rikici ya tashi a Najeriya zai iya shafarsu.

Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Hassan Maina Kaina.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG