Tun da tsakar daren jiya ne 'yan sandan a garin Kano suka kama buhunan makare da kuri'u a yankin Noman's Land na Unguwar Sabon Gari a cikin birnin Kano.
Tuni dai Jam'iyyar APC a jihar Jigawa ta nesanta kanta da lamarin, Alhaji Habibu Sani Sara, shine shugaban riko na Jam'iyyar APC a Jigawa, ya tabbatar da cewa basu da masaniya akan wannan batu kuma zasu gudanar da nasu binciken.
Al’amarin dai ya ja hankalin shugabannin Jam'iyyar PDP a Jigawa, inda tun a daren na jiya wata tawaga daga ofishin Jam'iyyar ta isa ofishin yankin na 'yan sanda wato Metro tare da neman 'yan sandan su fito da abin dake cikin buhunan, duk da cewa daga bisani 'yan sandan sun sanar dasu cewa, kuri'un na gwaji ne kawai.
Alhaji Umar Danjani Hadejia shine shugaban kwamitin yakin neman zaben dan takarar gwamna na PDP mai kula da harkokin matasa. Ya ce idan an ce kuri’un na gwaji ne, me ya sa aka kamasu su, kuma me ya sa sai da tsakar dare aka fito da buhunan. Don haka ba inda zasu sai sun ga abinda ya turewa buzu nadi.
Alhaji Garba Lawan dake zaman kakakin hukumar zabe ta kasa a nan Kano ya yi karin haske dangane da mutanen dake da hurumin rarraba takardar gwaji ta yin zabe a matsayin wayar da kan jama'a.
Yanzu haka dai rundunar 'yan sandan ta Kano na ci gaba da bincike akan wannan batu, a cewar kakakinta DSP Haruna Abdullahi.
Ga karin bayani cikin sauti.
Facebook Forum