A cakin hirar ta da Sashen Hausa, Hajiya Titi tace sau da dama ‘yan siyasa suna amfani da matasa ‘ya’yan talakawa a lokalin zabe wajen yin ayyukan asha da bangar siyasa. Ta kuma shawarci matasa su kiyaye doka da oda a lokacin zabe tare da shawartarsu su fito su zabi wanda ransu ke so, wanda kuma suke gani zai yi masu aiki ya inganta rayuwarsu.
Uwargidan tsohon mataimakin shugaban kasar, ta kuma yi kira ga mata su sa ido a kan ‘ya’yansu domin ganin basu dauki matakin da zai cuci rayuwarsu a lokutan zabe ba, yayinda ta yi kira garesu su fita kwansu da kwarkwatarsu ranar zabe domin kada kuri’arsu.
Hajiya Amina Titi tace ‘yan Najeriya suna da ‘yancin zabar wanda zai shugabance su da kuma sauya shugaban bayan shekaru hudu idan bai yi masu aiki ba.
Dangane da takarar maigidanta, Alhaji Atiku Abubakar, Hajiya Titi tace gwaggwarmayar da ya sha da kuma girma dikin talauci da ya yi, yasa ta hakikanta cewa zai zama shugaban kasa da zai inganta rayuwar talakawa. Ta jadada cewa, shi mai çıka alkawari ne sabili da haka, bata da shakka zai çıka alkawarin da ya yi na ba mata kashi talatin cikin dari, yayinda zai ba matasa kashi arba’in cikin dari na mukaman gwamnati.
Saurari cikakkar hirar da Alheri Grace Abdu ta yi da ita.
Facebook Forum